A ganawarsa da jakadan tarayyar Nigeriya a kasar Iran a birnin Tehran a jiya Litinin; Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin siyasar nahiyar Afrika da kasashen Larabawa Husain Amir-Abdullahiyan ya bayyana shirin Jamhuriyar Musulunci ta Iran na taimakawa a fagen kokarin da ake yi na ‘yantar da ‘yan mata dalibai da aka sace a tarayyar Nigeriya.
A nashi bangaren jakadan Nigeriya a kasar Iran Alhaji Tukur Mani ya bayyana godiyar Nigeriya ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran kan irin goyon bayan da take bai wa kasashen nahiyar Afrika musamman nuna damuwarta kan duk wani abin da ya shafi al’ummar Afrika tare da yin Allah wadai da ayyukan ta’addancin da ke addabarsu.
Tun a ranar 14 ga watan Aprilun da ya gabata ne ‘yan kungiyar Boko Haram suka kai hari kan garin Chibok da ke jihar Borno a arewa maso gabashin tarayyar Nigeriya tare da yin awungaba da ‘yan mata daliban makarantar sakandare fiye da 270 kuma har yanzu babu labarinsu.ABNA